Connect with us

Labarai

Yan Najeriya 98 ne suka mutu a hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu

Published

on

Akalla ’yan Najeriya 98 ne suka mutu a hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu tun daga shekarar 2022, a cewar gwamnatin Najeriya.

 

Haka kuma, kusan mutum 1,500 aka tilasta musu tserewa daga ƙasar bayan an lalata gidajensu da dukiyoyinsu.

A wata ganawa da aka yi a Abuja, ƙaramin ministan Harkokin wajen Najeriya, Sola Enikanolaiye, ya zargi Afirka ta Kudu da gaza kare ’yan Najeriya da sauran baƙi a ƙasar.

 

Ya ce da dama daga cikin waɗanda aka kashe ko suka jikkata mazauna ƙasar ne bisa ka’ida, yana mai allawadai da abin da ya kira ci gaba da hare-haren ƙyamar baƙi.

 

Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta musanta goyon bayan ƙyamar baƙi, inda ministan hulɗar ƙasa da ƙasa, Lamola, ya ce an kama wasu da ake zargi da kai hare-haren kuma za a gurfanar da su a kotu.

 

Ƙasashen biyu sun amince da ƙara tattaunawa kan batutuwan tsaro da hijira domin kare dangantakarsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!