Connect with us

Labarai

Kano: Majalisar Dokoki ta bukaci gwamnati ta zamanantar da asibitin Sabo Bakin Zuwo

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Gwamnati da ta zamantar asibitin Sabo Bakin Zuwo da aka fi sa ni da asibitin Jakara.

 

Ɗan majalisar jiha mai wakiltar Birni, Nabil Sarki Aliyu Daneji ne ya gabatar da ƙudirin a zaman majalisar na jiya Litinin.

 

Nabill Sarki Aliyu Daneji, ya bayyana cewa asibitin yana bukatar a samar masa da kayan aikin lafiya na zamani, la’akari da muhimmiyar rawar da asibitin ke takawa wajen kula da lafiyar al’ummar ƙaramar hukumar Birni.

 

A dai zaman majalisar, Wakilin ƙaramar hukumar Ungogo, Sa’ad Aminu Sa’ad, ya gabatar da kudiri inda ya bukaci gwamnati da ta kafa cibiyoyin koyar da sana’o’i a kananan hukumomin Kano 44, baya ga samar da irin su a Tudun Fulani da Zango a ƙaramar hukumarsa ta Ungogo.

 

Majalisar ta kuma buƙaci kwamitin kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu da ya gabatar da rahoton kan matsalar tsaro a Tsanyawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!