Kiwon Lafiya
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa zasu gudanar da taron gaggawa
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa zai gudanar da taron gaggawa yau a Abuja domin tattauna batutuwa da ke alaka da sauya lokacin gudanar da zabe da kuma wasu batutuwan na daban.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa taron ya biyo bayan dage babban zaben kasar nan da hukumar zabe ta kasa INEC tayi wanda aka shirya tun fari za a yi a ranar Asabar da ta wuce 16 ga wannan wata na Fabrairu da kuma biyu ga watan gobe na Maris.
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC ya kunshi shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo da kuma tsofaffin gwamnonin jam’iyyar da kuma gwamnonin da suke kan mulki na Jam’iyyar ta APC.
A daren juma’ar da ta wuce ne dai a wanni kafin a fara gudanar da zabukan, shugaban hukumar zabe na kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya bada sanarwar dage babban zaben.
Mahmood Yakubu ya ce dage zaben ya biyo bayan wani taron gaggawa da kwamishinonin hukumar suka gudanar bisa rashin isar kayan zabe zuwa wasu jihohin kasar nan a kan lokaci.