Connect with us

Labarai

Kwankwaso ya amince da matakin NDC na mika takarar shugabancin kasa a Kudancin Najeriya

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce ya goyi bayan matakin da jam’iyyar NDC ta yanke na keɓe tikitin takarar shugaban Najeriya a 2027 zuwa yankin Kudancin ƙasar,

Kwankwaso ya ce matakin ya nuna yadda jam’iyyar ke raba madafun iko da kuma tabbatar da adalci.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya yi jawabi ga wakilai da magoya bayansa da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Ya ce, “Ina goyon bayan matakin keɓe tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa Kudu domin yankin ya kammala shekarunsa takwas.

“Wannan ita ce matsayar jam’iyyar kan tsarin karɓa-karɓa.”

Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da magoya bayan NDC su wayar da kan al’umma game da manufofin jam’iyyar a yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Kalaman nasa na zuwa ne jim kaɗan bayan da NDC ta amince da miƙa tikitin takarar shugaban ƙasar a shekarar 2027 a Kudancin Najeriya na tsawon shekaru huɗu kawai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!