Labarai
Rundunar Anti Phone Snatching ta sanar da dakatar da ayyukanta a Kano

Hukumar da ke yaƙi da kwacen waya ta Anti Phone Snatching ta sanar da dakatar da ayyukanta baki ɗaya a faɗin jihar Kano, sakamakon abin da ta bayyana da rashin biyansu haƙƙoƙinsu na tsawon shekaru.
Mambobin ƙungiyar sun bayyana hakan ne a zantawarsa su da manema labarai, inda suka nuna damuwarsu kan halin da suke ciki duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da masu kwacen waya da sauran masu aikata laifuka.
Hukumar ta ce matakin dakatar da aikin da ta ɗauka zai ci gaba har sai gwamnatin ko hukumomin da abin ya shafa sun biya su haƙƙoƙinsu tare da duba koken da suke yi.
You must be logged in to post a comment Login