Connect with us

Labarai

Kwara: Amnesty ta bukaci a yi bincike kan rasuwar Fulani 150

Published

on

Kungiyar kare hakkin Dan-adam ta Amnesty International ta bukaci hukumomin kasar nan su binciki mutuwar Fulani akalla 150 a wani sansani a Jihar Kwara.

 

Ta ce kimanin mutane 1,500, ciki har da yara da mata masu juna biyu, ana tsare da su a sansanin ‘yan hidimar kasa na Yikpata bayan sun gudu daga hare-hare a wasu kananan hukumomi.

 

Kungiyar ta nuna cewa an tsare su na watanni cikin mawuyacin hali, inda ake fama da cunkoso da yunwa da rashin tsafta da kuma karancin kulawar lafiya, lamarin da ya haddasa mace-mace.

 

Wasu daga cikin wadanda aka tsare sun ce sun rasa ‘yan uwansu a sansanin.

 

Kungiyar ta kuma zargi jami’an tsaro da tauye hakkin jama’a, ciki har da hana su ‘yancin motsi da kuma nuna wariya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!