Connect with us

Labarai

INEC ta sanar da ranar yin zabukan cike gurbi na kujerun majalisar tarayya

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar da ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026 domin gudanar da zabukan cike gurbi na kujerun majalisu da suka zama babu kowa a kai a jihohi shida da suka hada da Kebbi da Kano da Ondo da Rivers sai Nasarawa da kuma Enugu.

 

A cewar hukumar, kujerun Sanatoci guda hudu ne za a cike, kana za a gudanar da zaben cike gurbi na kujera guda daya ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano, da kuma kujera guda daya ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi.

 

INEC ta bayyana cewa za a gudanar da wadannan zabuka ne a rana guda da zaben gwamnan Jihar Ekiti da aka shirya yi a ranar 20 ga Yuni, 2026.

 

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana jadawalin zaben yayin rantsar da sabuwar Kwamishinar Kasa, Rear Admiral Jamila Malafa mai ritaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!