Connect with us

Labarai

Amnesty ta yi Allah-wadai da kashe mutane 17 a harin ‘yan bindiga a Sokoto

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan aƙalla mutane 17 da ‘yan bindiga suka yi a ƙauyen Dangulbi da ke ƙaramar hukumar Tureta a Jihar Sokoto ranar 1 ga Yunin 2026. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai mutanen da suka dawo gida domin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah.

 

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata, ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike cikin gaggawa kan harin, su tabbatar an kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban shari’a. Amnesty ta kuma bukaci gwamnati ta ƙara matakan tsaro ga al’ummomin karkara da ke fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga.

 

Rahotanni daga mazauna yankin sun ce ɗaruruwan ‘yan bindiga masu ɗauke da makamai a kan babura sun mamaye Dangulbi da safe, inda suka fara harbe-harbe, suka wawushe shaguna tare da tilasta wa mazauna guduwa zuwa dazuka domin neman mafaka. An ce maharan sun shiga garin ne tsakanin ƙarfe 10 zuwa 11 na safe bayan sun fito daga wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara.

 

Ƙungiyar Amnesty ta ce wannan hari ya sake nuna gazawar hukumomi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan da ke fama da matsalar tsaro. Ta jaddada cewa hare-haren da ake ci gaba da kai wa a gabashin Sokoto da maƙwabtanta suna haddasa asarar rayuka, garkuwa da mutane da kuma raba dubban mutane da muhallansu. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta jihohi su ɗauki matakan gaggawa da dorewa domin hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!