Labarai
kwararru a harkar kiwon lafiya sun ja hankalin gwamnati kan kara kaimi wajen daukar sabbin ma’aikatan lafiya
Mataimakin Shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ya ja hankalin Gwamnatin jihar Kano wajen kara kaimi ta fuskar daukar sabbin ma’aikatan lafiya da likitoci.
Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin babban taron likitoci masu fida na duniya karo na 53 da ake gudanarwa anan jihar Kano.
Ya ce la’akari da yadda ake samun karuwar marsa lafiya a asibitoci musamman a yankunan karkara, akwai bukatar a samar da Karin kayayyakin aiki da magunguna baya ga gina asibitoci da kuma Karin ma’aikatan lafiya.
Da yake jawabi tun da fari, wani kwararren likitan mafitsara daga asibitin koyarwa na Aminu Kano Dakta Muzammbil Abdullahi yace sun zabi kananan hukumomin Dambatta don yin ayyukan fida da suka shafi Gwaiwa da Kaba sai kuma Dawakin Tofa don yin aikin ido, duk don tallafawa mutanen dake yankunan.
Kimanin mutane fiye da 1500 aka duba tare da basu magunguna kan cutuka daban-dabam a Dawakin Tofa tare yiwa wasu fiye da 50 aikin ido, sai kuma fiye da mutane dari suka amfana da aikin cire kari a wani mataki na saukake wa al’ummar wannan yankunan wahalhalun kasha kudade wajen neman lafiya.