Connect with us

Coronavirus

Labari mara dadi: Wadanda suka kamu da Corona sun haura 500 a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa an samu karin mutane 65 da suka ku da cutar Covid-19 a ranar Jumu’a.

Wannan kari da aka samu ya kai jimillar masu dauke da cutar a jihar zuwa 547.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an samu karin mutum 5 da suka rigamu gidan gaskiya sanadiyyar cutar a ranar jumu’ar.

Adadin wadanda cutar ta hallaka a Kano ya kai mutum 18.

Har ila yau, a ranar an jumu’ar an sallami mutum 1 da ya warke daga cutar, wanda ya kai adadin wadanda suka warke zuwa mutum 20.

Karin Labarai:

Ma’aikatan jinya 18 sun kamu da Corona a Kano

An sallami mutum 6 da suka warke daga Corona a Kano

Yazuwa yanzu ragowar mutane 509 dake dauke da cutar na cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar ta Covid-19 dake Kano.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da aka sallami kwamishinan lafiya na jihar Kanon, cikin kunshin mutane 6 daga cikin ‘yan kwamitin yaki da cutar Covid-19 a jihar da suka kamu da cutar bayan sakamakon gwajin da akayi musu har sau biyu ya nuna cewa basa dauke da cutar a halin yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,220 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!