Connect with us

Coronavirus

Ma’aikatan jinya 18 sun kamu da Corona a Kano

Published

on

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta jihar Kanoano tace ma’aikatan su 18 ne suka kamu da cutar Covid-19 ba tare da sun sani ba a yayin da suke tsaka da ayyukan ceton rayukan al’umma.

Shugaban kungiyar Ibrahim Maikarfi Muhammad ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu Abba Isah Muhammad, inda ya ce sun yiwa ma’aikatansu 188 gwajin cutar Corona wanda sakamakonsu ya tabbatar da cewa mutum 18 na dauke da cutar.

Maikarfi Muhammad yace ma’aikatansu ne kan gaba wajen saurin kamuwa da cutar matukar gwamnati bata samar musu da isassun kayan kariya ba.

Karin labarai:

An sallami mutum 6 da suka warke daga Corona a Kano

Corona ta hallaka mutane 13 a Kano

Wannan yana zuwa ne kwana guda bayan da kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da cewa mambobinta 34 ne suka kamu da cutar ta Covid-19 a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!