Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An sallami mutum 6 da suka warke daga Corona a Kano

Published

on

Hukumomi a jihar Kano sun tabbatar da cewa an sallami mutane 6 wadanda suka warke daga cutar Covid-19 a jihar.

A jadawalin masu dauke da cutar da ma’aikatar lafiya ta jihar Kanon ta wallafa a shafinta na Twitter a daren Laraba ta ce an sallami karin mutum 3 da suka warke daga cutar wanda adadin wadanda suka warke ya kai 6 a jihar.

Izuwa yanzu mutane 427 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Covid-19 a Kano.

Mutane 13 daga ciki sun rigamu gidan gaskiya sanadiyyar cutar ta Covid-19.

Karin labarai:

Corona ta hallaka mutane 13 a Kano

Masu Corona sun haura 400 a Kano

A yau Alhamis itace daya daga cikin ranaku biyu da gwamnatin Kano ta sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar.

Idan zaku iya tunawa dai a Talatarnan ne aka samu dai-daito tsakanin gwamnatin Kano da ‘yan Kasuwa a jihar kan karin kayan masarufi musamman a ranakun da aka sassauta dokar kulle saboda Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!