Kiwon Lafiya
Lafiya: Mata na fuskantar barazanar kamuwa da cutuka lokacin al’ada
Wata kwararriyar likitar mata a asibiti Amiu Kano Dakta Zainab Datti Ahmad ta ce, rashin tsaftace jiki lokacin al’ada ga Yaya Mata shi ne ke haifar musu da bakin cututtuka a wannan lokaci.
Dakta Zainab Datti Ahmad ta bayyana hakan yayin Taron wayar da kan Mata kan yadda za su kula da tsaftar jikin su musamman a lokacin jinin al’ada a wani bangare na makon bikin al’ada da ake gudanarwa wanda Gidauniyar Widi Jalo Foundation ta gudanar.
A cewar likitar wajibi ne ga matan da suke yin al’ada duk lokacin da za su shiga bandaki ya zamana suna tsaftaceshi tahanyar amfani da sinadaren dake kashe cutuka.
Haka Kuma ta ce, duba da rashin kudi a hannun Mutane mace za ta iya amfani da Toka wajen wanke bandake idan za ta shiga, tare da yin amfani da Lalle da Ruwan da aka jika Toka da Kuma Alimun wajen wanke jiki.
Da yake jawabi shugaban Gidauniyar ta WIDI JALO Alhaji Abubakar WIDI, da Jami’ar Gidauniyar a nan Kano Hajiya Bilkisu Hamisu Mai Iyali tayi magana a madadin SA ta ce duba da wahalar da Mata suke Sha lokacin jinin al’ada na Rashin abin da za su kula da kan su yasa suka shirya musu bitar.
Yayin bitar ta wuni guda Likitoci da daliban kiwon Lafiya daga Asibitocin jihar Kano da dama ne suka gabatar da jawabai kan yadda Mata za su kula da kansu lokacin jinin al’ada.
You must be logged in to post a comment Login