Kiwon Lafiya
Lagos:mutane 18 sun rasa rayukansu sakamakon rushewar gini
Kimanin mutane 18 ne suka rasa rayukansu a yayin da wani gini mai hawa hudu ya rufto a yankin Island da ke jihar Ikko inda kimanin mutane 41 ne suka samu raunuku.
Hatsarin ya afku da misalin karfe 10 na safe akan titin unguwar Massey wanda ya ke daura da Oja Ita-Faaji, rahotanni dai na nuni da cewa hawa na uku na benen na dauke da wata makarantar firamare da ya rufto inda wasu yan makarantar suka makale a ginin.
Kwamishinan lafiya na jihar Lagos , Jide Idris ya tabbatar da faruwar haka, yana mai cewa tuni aka kai wa wadanda hatsari ya rutsa da su babban asibiti na jihar yayin da kuma aka kai su abisitin nkoyarwa na jihar ta Lagos.
Rahotanni sun bayyana cewar an samu karancin jini a babban asibitin jihar inda aka kai da dama daga cikin wadanda abin ya rutsa da su , bayan da gwamnatin jihar tayi kira ga al’ummar jihar da su kawo agajin jini.
Kwamishinan lafiyar ya ce za’a cigaba da kai agaji inda abun ya faru domin ceto wadanda suka makale a cikin baraguran gini.
Hukumar bada agaji na gaggawa ta jihar ta ce fiye da mutane 41 ne suka rauni a ginin
A dai shekara ta 2014 ne aka sanyawa ginin alamar a rushe ginin makarantar baki daya, amma kuma aka gaza yin hakan.
Wani da abun ya faru akan idanunsa ya ce makamancin wannan al’amari ya faru a shekarar da ta gabata, sakamakon gidajen da gwamnati ta sanya alama da rushe su, suka ki amincewa da matakin.