Labaran Wasanni
Laliga: Barcelona ta sha da kyar a hannun Granada

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi kunnan Doki da Granada a gasar cin kofin Laligar kasar Spain da ci 1-1.
Mintuna 2 da fara wasan dan wasan kungiyar Granada, Domingos Duarte ya zurawa kungiyar tasa kwallo bayan taimako da ya samu ta hannun dan wasa Sergio Escudero.
Sai a mintuna na 90 Dan wasan Barcelona Ronald Araujo ya farke kwallon bayan taimako da ya samu ta hannun dan wasa Pablo Gavira.
Hakan yasa aka tashi wasan da ci 1-1 a gasar ta Laligar kasar Spain mako na 5.
You must be logged in to post a comment Login