Labaran Kano
Lauya: zamu yi duk mai yiwuwa domin kwatowa dattijo hakkinsa
Wani lauya mai rajin ceton al’umma a jihar Kano Barista Abba Hikima Fagge, ya bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen kwatowa wani dattijo da aka kashe dansa hakkinsa.
Lauyan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Freedom Radio, yana mai cewa zai yi iya yinsa wajen bin kadun matashin wanda ake zargin wani DPO da ake yiwa lakabi da Kwanta-Kwanta ya kashe shi kimanin shekaru 20 da suka gabata.
Kimanin shekaru 20 kenan gawar matashin ke ajiye a dakin adana gawar waki na asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda mahaifim nasa ya ce ba zai taba binne gawar ba har sai an yi masa adalci.
Barista Abba Hikima ya kara da cewa, sashe na 33 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya bada damar bin hakki a shari’ance duk tsawon lokacin da aka dauka da fara bibiyar hakkin.
A zantawar Freedom Radio da mahaifin yaron, ya bayyana cewa tun a wancan lokacin, sun yi ta faman zuwa kotu, amma fa wanda ake zargi da kashe dan nasa bai taba halartar zaman kotun ba.