Labarai
Lauyoyi sun maka Shugaba Bola Tinubu da Nuhu Ribadu a kotu kan shirin samar da ƙungiyar Hisbah

Ƙungiyar Lauyoyi ‘yan asalin jihar Kano ta maka Shugaba Bola Tinubu da Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa NSA, Mallam Nuhu Ribadu, a kotu kan shirin samar da wata ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta a Kano mai kama da wacce ake da ita a jihar, tana mai gargadin cewa, matakin zai iya barazana ga zaman lafiya da tsaro da ake da shi a jihar.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata takardar mai dauke da sa hannun Shugabanta Malam Usman Imam Tudun Wazirchi, da Sakatariyarta ta Ƙasa, Rita Benedict,.
Ta cikin sanarwar, lauyoyin sun yi zargin cewa ɗaukar jami’an sabuwar ƙungiyar Hisba din mai zaman kanta wani ɓangare ne na siyasa da ka iya wargaza zaman lafiyar jihar Kano, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Wannan matakin ya biyo bayan fitar da fom din daukar jami’ai 12,000 na hukumar Hisbah mai zaman kanta da ake shirin ƙirƙira a karshen makon da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login