Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Lawan, Femi ga gwamnonin kudu: Ku bai wa kananan hukumomi ƴanci kafin neman fasalta kasa

Published

on

Shugaban majalisar dattijai sanata Ahmed Lawan da takwaransa na wakilai Femi Gbajabiamila sun soki gwamnonin yankin kudancin ƙasar nan goma sha bakwai wadanda su ka yi kiran da a sake fasalta ƙasar nan.

 

A cewar shugabannin majalisun dokokin tarayyar ba daidai bane ace zababbun shugabanni sune za su rika furta irin wannan kalamai da kowa ya san na siyasa ne.

 

Sanata Ahmed Lawan ya ce kowa ya san cewa matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan tana alaka ne da rashin bin tsarin ƙananan hukumomi mai kyau, inda shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya yi batun cewa, batun neman sake fasalta ƙasa zai iya zama yana bisa ka’ida amma ba zababbun shugabanni musamman gwamnoni ne ya kamata su jagoranci wannan batu ba domin kuwa inda da gaske su ke yi to su fara fasalta jihohinsu tukunnna.

 

Femi Gbajabiamila ya ce halin da ake ciki a yanzu ba ya bukatar nuna wa wani ɗan ƙasa yatsa maimakon haka kamata ya yi ƙasar gaba ɗaya ta hade wajen neman mafita kan halin da ake ciki.

 

A cewar Femi Gbajabiamila babu wani mutum da zai koma gefe yana nuna yatsa ma wasu kamar shi na gari ne domin kuwa kowa ya taimaka wajen tabarbarewar halin da ake ciki a yanzu.

 

Shugabannin majalisun dokokin tarayyar sun bayyana hakan ne jim kadan bayan sun halarci sallar idi a masallacin fadar shugaban ƙasa a jiya alhamis

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!