Labaran Wasanni
LMC: An saka sharuda ga kungiyoyi a kan dawowa gasar
Kamfanin shirya gasar League ta kasa LMC, ya fitar da jerin ka’idoji ga kungiyoyin kwallon kafa na cikin gida dake fafatawa a gasar cin kofin kwararru ta kasa a ya yin da ake tunkarar kakar wasanni ta 2020/2021.
A cikin jerin dokokin gasar ta kasa, LMC ya saka dokar cewa dole sai kungiyar da ta mallaki kudi akalla Naira miliyan 200 tare da kuma yi wa ‘yan wasan ta da ma’aikatanta rijistar Inshora, kafin a fara gudanar da gasar a wata mai kamawa.
LMC ya kara da cewa, ya zama dole kafatanin kungiyoyin su kiyaye ka’idojin kariya ga kamuwa da cutar COVID-19.
A dai ranar Litinin da ta gabata ne, kamfanin ya baiwa kungiyoyin 20 umarnin kawo takardun neman lasisi da gwamnatin tarayya ta tilasta ga kungiyoyin.
Haka zalika, LMC ya bukaci masu horas da kungiyoyin da su gabatar da bayyanan shaidar mallakar Naira miliyan 200 wanda shi ne abu mai muhimmanci kafin a amince wa kowace kungiya shiga gasar ta cin kofin kwararru ta kasa.
You must be logged in to post a comment Login