Labaran Wasanni
LMC ta ci tarar Kano Pillars tare da dakatar da shugaban ta Jambul
Kamfanin shirya gasar Premier League ta Najeriya LMC, ya kori shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Alhaji Surajo Shuaibu Jambul kwata-kwata daga gasar bayan zargin naushin mataimakin Alƙalin wasa a fafatawa tsakanin Pillars da Dakkada, kwantan wasan mako na 31 na gasar NPFL, da aka fafata a ranar Alhamis 23 ga Yuni 2022.
Haka zalika , kamfanin na LMC ,yaci tarar Ƙungiyar Naira Miliyan Biyu , da kuma yiwuwar ƙwace mata maki uku a gaba in haka ta ƙara faruwa a wasannin ta na gaba.
Cikin hukuncin na LMC, tawagar ta Pillars za ta biya jami’in kamfanin shirya gasar Firimiyar LMC, Uchenna Iyoke Naira 500,000 sakamakon lalata masa kayan aiki, da akayi a hatsaniyar da ta faru a wasan, wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata ba tare da ‘yan Kallo ba.
You must be logged in to post a comment Login