Connect with us

Coronavirus

Lock Down: Wani Dan sanda ya koma taya matarsa aikin gida a Kano

Published

on

Yayinda dokar kulle da zaman gida ke cigaba da gudana a wasu jihohin kasar nan ciki harda jihar Kano, sai gashi wani jami’in dan sanda a nan Kano yayi amfani da wannan damar wajen taya uwargidansa ayyukan gida.

Wannan jami’in dan sanda mai suna Shu’aibu M. Babangida ya wallafa wasu hotunansa guda biyu a shafinsa na Facebook wanda ke nuna shi yana gyaran Salak.

Wannan dai na zuwa ne yayinda wasu matan ke kukan cewa basa samun kulawa yadda yakamata daga mazajensu a yayin wannan zaman gida na “Lock Down”.

Ko a ranar Asabar wakiliyarmu Aisha Kabara ta zanta da wasu iyaye mata a kwaryar birnin Kano wasu daga ciki suka ce babban kalubalensu shi ne yadda mazajensu basa komai sai dai sanyasu aiki dauko wancan ajiye wancan.

Su kuwa wasu cewa su kai, batun buda baki shi ne ke ci musu tuwo a kwarya domin yanzu basa samun koda dankalun hausa su soya, yanzu kuwa sai dai kawai ayi amfani da abinda ya samu.

To da fatan mazaje za su yi koyi da wannan jami’in dan sanda.

Karin labarai:

Malaman Addinin Musulunci sun yabawa Kwamishinan ‘’Yansandan jahar Kano.

Rundunar yan sandan Kano ta yi holin mutane 116 da ake zargi da manyan laifuka

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!