Labarai
Ma’aikatan Freedom radiyo sun fara karbar horo
Tashar Freedom rediyo tare da hadin gwiwar tashar Dala FM, sun gudanar da horar da ma’aikatan su domin sanin hanyoyin gudanar da ingantaccen aikin jarida don jin dadin mai sauraro.
An dai fara gabatar da horon da ma’aikatan ne a safiyar yau Talata ya yin da manajan tashar Freedom radiyo Kano Ado Sa’idu Warawa ya gabatar da mukala kan gogar da ma’aikata yadda za su gudanar da ayyukan su na aikin jarida.
Taron wanda aka yi masa take da na ”Karawa juna sani” an gudanar da shi ne karkashin kulawar mataimakin Janaral manaja Adamu Isma’il Garki, ya yin da Janaral manaja mai kula da ayyukan Injiniyoyi na tashar Injiya Jamilu Ibrahim ya dafa masa.
Daga cikin ma’aikatan da aka suka halarci horon, akwai Manajan sashin yada labarai na tashar Freedom radiyo Kano, Malam Nasiru Salisu Zango da Manajar shirye-shirye a Freedom Kano, Aisha Bello Mahmod, sai kuma manajan tashar Dala FM, Malam Garzali Yakubu.
You must be logged in to post a comment Login