Kaduna
Ma’aikatan Shari’a sun tsunduma yajin aiki a Kaduna

An rufe dukkan kotunan jihar Kaduna a ranar Litinin bayan kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani domin neman aiwatar da cikakken baiwa ɓangaren Shari’a ƴancin biyan albashi ga ma’aikatan ta da wasu buƙatu na albashi.
JUSUN ta ce matakin ya biyo bayan gazawar da gwamnatin jihar tayi wajen amsa wasikun korafi da ƙungiyar ta aike mata tun daga watan Satumba.
Bayanan sun nuna cewa kotunan jiha da na tarayya, na Shari’a da na al’ada duk an rufe su, yayin da wasu ma’aikata ke taimakawa jama’a wajen samun takardun rantsuwa a wajen kotunan.
Ƙungiyar ta lissafo bukatunta da suka haɗa da biyan bashin albashi da gyaran matakan albashin, da kuma biyan kudaden hutu da sufuri da suka taru tun daga shekarar 2016.
An ce an yanke shawarar fara yajin aikin ne tun bayan taron gaggawa da JUSUN ta gudanar a ranar 13 ga Oktoba.
You must be logged in to post a comment Login