Labaran Kano
Ma’aikatar kananan hukumomi ta gabatar da kasafin kudi na naira biliyan dari biyu
Ma’aikatar kananan hukumomin ta jihar Kano ta gabatar da naira biliyan dari biyu da goma sha shida da miliyan sittin da biyu da dubu dari tara da sabain da uku da dari daya da talatin da shida da Kwabo arbain da hudu a matsayin kunshin kasafin kudin kananan hukumomin jihohi arbain da hudu.
Hakan ya biyo bayan karanta wasikar da ma’aikatar kananan hukumomi ta aikewa majalisar mai dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar Murtala Sule Garo wanda mataimakin shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta da safiyar yau.
Ta cikin wasikar dai mataimakin shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari, ya ce ma’aikatar kananan hukumomin ta ce kunshin kasafin kudin kananan hukumomin ya dace da bukatun al’ummar jihar Kano.
Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma baiwa kwamitocin ta da ke kula da kasafin kudi da Kuma na kananan hukumomi wa’adin makwanni hudu da su je su tsestsefe kunshin kasafin kudin kafin su dawo da shi ga majalisar