Kiwon Lafiya
Ma’aikatar Lafiya ta Kano ta nuna damuwa kan rashin ingantattun ma’aikata a aikin rigakafin Rubella

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bayyana damuwa kan yadda wasu daga cikin ma’aikatan da ke aikin rigakafin cututtukan Measles da Rubella ke gudanar da ayyukansu, inda aka gano rashin inganci da kwarewa wajen aiwatar da ayyukan su a sassa daban-daban na jihar. Ma’aikatar ta ce daga yanzu ba za ta kara yarda da tura ma’aikatan da ba su da horo ko cancanta ba domin irin wadannan muhimman ayyuka ba.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada cewa kawai ma’aikatan da suka samu horo da kwarewa ne za su ci gaba da gudanar da aikin rigakafin, domin tabbatar da inganci, gaskiya da kuma kiyaye lafiyar jama’a. Ya kuma gargadi hukumomin kananan hukumomi da su guji sakaci ko rashin kulawa wajen gudanar da aikin, yana mai cewa Ma’aikatar ba za ta lamunci kasala ko sakaci ba daga kowane bangare.
Haka kuma, Kwamishinan ya bukaci shugabannin kananan hukumomi da su dauki nauyin wannan kamfen din sosai, tare da tabbatar da kulawa da sa ido yadda ya kamata kan dukkan ma’aikatan da ke aiki a yankunansu. Ya kuma jaddada cewa Ma’aikatar Lafiya za ta ci gaba da jajircewa wajen kare lafiyar jama’a da tabbatar da nagartar ayyukan rigakafi a jihar.
A karshe, Dr. Yusuf ya yi kira ga dukkan ma’aikatan lafiya da su kasance masu jajircewa da kwarewa a lokacin gudanar da aikin, yana mai cewa kare lafiyar al’umma abu ne da ya rataya a wuyan kowa. Ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri da hadin kai wajen ganin an cimma nasarar wannan kamfen din rigakafi da ake gudanarwa a halin yanzu.
You must be logged in to post a comment Login