Labarai
Ma’aikatar ruwa sha ta kasa ta musanta zargin sayar da madatsan kasar
Ma’aikatar ruwan sha ta kasa Sha ta karya ta ikirarin da wasu ke yi cewa ma’aikatar na shirin saida madatsan kasar na ba gaskiya ba ne, sai dai a cewar ma’ikatar ana shirin jinginar da tashar sarrafa makamashi wajen samar da ruwan sha na madatsun ruwa ne kawai.
Ministan albarkatun ruwa Suleman Adamu ya bayyana hakan a yayin da yake bude taron karawa juna sani na manema labarai kan ruwan sha a birnin tarayya Abuja.
A cewar ministan abunda aka yi ko shirin da ma’aikatar ke niyyar yi shi ne jinginar tashoshin sarrafa makamishin na madatsun don bunkasa harkokin su ga ‘yan Najeriya don cin gajiyar su, amma gwamnatin tarayya ita ce ke mallake da su.
Suleman Adamu ya ce shirin jinginar da tashar makamashin wanda hukumar da ke kula da jininar da kadarorin gwamnati ta kasa da kuma hukumar dake kula da saida kadarorin gwamnati ta kasa su ne ke da alhakin duba yuwar shirin da kuma lokacin da za’a a dauka wajen jinginar da tashar sarrafa makamashin don samun ruwan sha.
Haka zalika Ministan na ruwan sha ya kara da cewar makasudun daukar wannnan matakin da ma’aikatar ta yi shi ne don baiwa kamfanonin dake tunkuda wutar lantarki ga masu rarrabawa don amfani da shi.
Da yake Karin bayani kan madatsar ruwa ta Gurara, Suleman Adamu y ace ma’aikatar san a shirin samar da wata hadin gwiwa wajen, wanda zai yi dai-dai da dokar da hukumar da ke kula da jiginar da kadarori ta kasa ta shinfida wajen bunkasa matdatsar.