Connect with us

Labarai

Mai dakin Sir Abubakar Tafawa Balewa ta rasu a shekaru 85

Published

on

Rahotonni daga jihar Legas na cewa Allah ya yiwa Hajiya Aishatu Abubakar Tafawa Balewa uwar gidan marigayi firaministan kasar nan na farko, wato Alhaji Abubakar Tafawa Balewa.

Hajiya Aisha ta rasu tana mai shekaru 85, ta bar ‘ya’ya 6 daga cikinsu akwai Sadiq, Usman da kuma Hajiya Yalwa.

Nan gaba kadan ne za’a sanar da lokaci da kuma wurin da za’a yi jana’izar ta.

Muna fatan Allah ya jikanta ya gafarta mata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!