Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya na gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen kiwon lafiya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ce, ta na gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden kiwon lafiya, yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar magani da sauran kudaden jinya da suke biya daga aljihunsu.

 

Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIA, ta ce, gwamnatin tarayya ta fitar da Naira biliyan 235 ta hannun Asusun Samar da Kiwon Lafiya a matakin farko cikin shekaru uku.

 

Hukumar ta kuma bayyana cewa adadin mutanen da suka yi rajistar inshorar lafiya ya haura miliyan 23, amma har yanzu iyalai da dama na fuskantar matsalar tsadar kula da lafiya.

 

NHIA ta ce za a tattauna batun ne a wani taron kwana biyu da zai fara yau Litinin 28 ga Satumba, inda masana za su duba yadda za a yi amfani da kudaden kiwon lafiya yadda ya kamata, da kuma tabbatar da cewa karin kashe-kashen kudin gwamnati na haifar da ingantaccen sauyi ga al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!