Labarai
Majalisa: akwai bukatar sake nazarin kundin tsarin kasa
Majalisun dokokin kasar nan sun ce akwai bukatar sake nazartar kundin tsarin mulkin kasar nan ta yadda zai bada damar samar da ‘yan sandan jihohi, wanda majalisun ke ganin cewa zai kawo karshen rigingimu da kashe kashen da ke faruwa a sassan kasar nan.
Bukatar ta zo ne a zaman majalisun na jiya, inda suka ce tsarin harkokin tsaron kasar nan ya gaza, a don haka akwai bukatar a baiwa jihohin kasar nan damar kafa ‘yan sandan su.
Majalisun biyu sun amince da a sake nazartar kundin tsarin mulkin kasar nan domin cimma wannan manufa.
Bukatar sake nazartar kundin tsarin mulkin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan bindiga da ba’a san su ba suka harbe wasu ‘yan sanda 7 har lahira a daren ranar Litinin din da ta gabata a birnin Tarayyar Abuja .
Tuni majalisun suka kafa kwamitin da zai nazarci kundin tsarin mulkin wanda mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu zai jagoranta tare da gabatar da rahoton su cikin makwanni 2.