Kiwon Lafiya
Majalisa ta amince da dokar tilasta gwaji kafin aure a Kano
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar tilasta gwaji kafin aure, don takaita yaɗuwar cututtuka.
Majalisar ta ce, ta yi la’akari da yadda cututtukan da ke yaɗuwa tsakanin ma’aurata, a wasu lokutan ma har zuwa ƴaƴan su ke ƙara yaɗuwa, abinda ya tilasta mata amincewa da ƙudirin dokar.
Ɗan majalisa Musa Ali Kachako da ke wakiltar ƙaramar hukumar Takai a jihar Kanon wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin dokar ya ce, wajibi ne majalisar ta samar da wannan doka, don inganta lafiyar jama’a.
Wasu daga cikin al’ummar Kano sun yi maraba da wannan mataki na majalisar.
labarai masu alaka:
Ganduje ya gabatar da dokar kare kananan yara ta bana a gaban majalisar dokoki
Majalisar dokoki ta Kano ta nemi goyan bayan masarautar Bichi
Dama dai likitoci sun daɗe suna kira ga jama’a da su kaucewa yin aure kai tsaye ba tare da gwaji ba don sanin matakin lafiyar su.
Dr. Tijjani Nasir Na-gwamutse likita ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce, kowacce ƙasa da irin cututtukan da suka fi addabar mutanen ta da kuma irin yanayin su a don haka sai masu niyyar aure su yi la’akari da hakan wajen yin gwajin.
Cututtukan da suka fi yaɗuwa a tsakanin ma’aurata da ƴaƴan su matukar aka yi aure ba tare da gwaji ba, sun haɗar da cuta mai karya garkuwar jiki, da amosanin jinni wato sikila da kuma ciwon sanyi da dai suran su.
You must be logged in to post a comment Login