Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisa za ta binciki badakalar baiwa manoma rancen kudi

Published

on

Majalisar wakilai za ta binciki badakalar rashin raraba  kudade da ya tassama fiye da Naira biliyan 81 a wani banagare na shirin rarrabaawa manoma rance wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar a shekara ta 2015.

Matakin ya biyo bayan kudirin da dan Majalisa daga jihar Ogun Serguis Ose ya gabatar kan bukatar dake akwai na Majalisar ta binciki yada bankin manoma ya yi  amfani da kudaden da kuma yadda ya rarraba karkashin shirin baiwa manoma rance a kasar nan.

Dan majalisa Serguis Ose  ya ce alhakin babban bankin kasa ne CBN na kafa shirin baiwa manoma rance don bunkasa ayyukan su da nufin samar da fahimta tsakanin kamfanonin manoma dae cikin shirin da kuma kananan manoma.

A cewar sa makasudun shirin baiwa manoma rancen shi ne samar musu da basuka don bunkasa samar da abinci da ayyukan noma da suka hadar da Shinkafa da Rogo da dankali da doya da dawa da Gero da dai sauran su.

Kazalika dan Majalisar ya shedawa Majalisar cewa daga cikin kudaden da babban bankin kasar nan CBN ya fitar don aiwatar da shirin na baiwa manoma rance ya haura fiye da Naira biliyan dari da hydy da miliyan dari biyu da Ashirin da shida da dubu dari da casin da bayar da shida.

Amma kuma daga cikin kudaden an rabawa kamfanoni manoma dake sassan kasar nan fiye da Naira biliyan 86 sai dai wasu daga cikin manoman sun ce kawo yanzu basu amfana da wannan kudaden ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!