Labarai
Majalisar Dattawa na neman hana shigo da Yaduddukan Kasashen Waje

Majalisar Dattawa Ta Nemi Haramta Shigo da Yaduddukan Kasashen Waje Domin Farfado da Masana’antar Yadi
Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta haramta shigo da yaduddukan kasashen waje gaba daya, domin farfado da masana’antar yadi ta cikin gida da kuma bunkasa noman auduga a fadin kasar nan.
Haka kuma, majalisar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatun Noma da Kasuwanci da Zuba Jari da su dauki matakan gaggawa domin dawo da martabar masana’antun yadi a Najeriya, musamman a yankin masana’antu na Kaduna zuwa Kano.
Sanatocin sun bayyana cewa farfado da wadannan masana’antu zai samar da dubban ayyukan yi ga matasa, tare da taimakawa wajen rage matsalar rashin aikin yi da kuma kalubalen tsaro da ke addabar kasar.
Wannan kuduri ya samu amincewar majalisar ne bayan tattauna wata bukata mai taken “Gaggawar Farfado da Masana’antun Yadi a Najeriya, Musamman a Yankin Kaduna da Kano”, wadda Sanata Sunday Katung na jam’iyyar APC mai wakiltar Kaduna ta Kudu ya gabatar, tare da goyon bayan wasu sanatoci daga jam’iyyu daban-daban.
Sanatocin sun jaddada cewa dawo da masana’antar yadi zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, bunkasa masana’antu na cikin gida, da kuma rage dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga kasashen waje.
You must be logged in to post a comment Login