Labarai
Sojoji sun ceto mutane 360 da ’yan ta’adda suka sace a Borno

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai tare da dakaru na musamman sun ceto mutane 360, galibinsu mata da kananan yara, da ’yan ta’adda suka sace daga garin Ngoshe a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne a yankin tsaunukan Mandara a ranar 6 ga Yuni, inda aka samu nasarar kubutar da wadanda aka sace tun bayan harin da aka kai wa al’ummar Ngoshe a watan Maris.
Sai dai ya ce jarirai biyu sun rasu yayin aikin ceton sakamakon wahalar hanya. An kuma kai wadanda aka ceto asibiti domin kula da lafiyar su kafin a hada su da iyalan su.
You must be logged in to post a comment Login