Labarai
Majalisar dattawa ta amince da kudirin gyaran dokar hukumar FRSC

Majalisar dattawa ta amince da kudirin gyaran dokar hukumar kiyaye hadurra FRSC na shekarar 2026, wanda ya tanadi tarar Naira dubu 50 ga duk wanda kotu ta kama da laifin yin talla, kasuwanci ko wa’azi a cikin motocin haya.
Kudirin na da nufin rage abubuwan da ke haddasa hankalin direbobi ya rabu yayin tuki, tare da inganta tsaro da kare rayukan matafiya a kan manyan hanyoyin kasar nan.
To sai dai har yanzu kudirin bai zama doka ba, domin yana jiran amincewar Majalisar Wakilai da kuma sanya hannun Shugaban Kasa kafin a fara aiwatar da shi.
You must be logged in to post a comment Login