Connect with us

Labarai

Takaddama ta kaure tsakanin Hisbah da hukumar Tace Fina-Finai a Kano

Published

on

Takaddama ta kaure tsakanin hukumar Hisba da kuma hukumar Tace Fina-Finai game da sana’ar tura fina-finai wato downloading a jihar Kano.

Tun da farko  hukumar Hisbah ce ta fara sanar da haramta sana’ar bisa zargin cewa ana amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.

To sai dai hukumar Tace Fina-Finai ta yi fatali da wannan matakin tana mai cewa sana’ar halastacciya ce kuma ita ce ke da ikon yi ko hana sana’ar.

”Wannan mataki abu da ya kamata a ce mu da su mun zauna mun tattauna a kan makomar yin haka kasancewar mu ke da hurumi da doka ta ba mu na kula da masu wannan sana’a”, a cewar Abdullahi Sani Sulaiman kakakin hukumar.

”Akwai wani tsari da muka yi musu na rigima da suke samu tsakaninsu da masu shirya fina-finai da cewa ba za su sake ɗaukar fim ba, sai da sahalewar masu fina- finai,” in ji shi.

A nata ɓangare, hukumar Hisba ta ce ta ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-ƙorafe da dama da hukumar ta samu daga al’umma.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen ya shaida wa BBC cewa akwai masu fakewa da sana’ar suna tura wa jama’a hotuna da bidiyon tsiraici, lamarin da ya ce na matuƙar gurɓata tarbiya.

”Ana samun wasu ɓata-gari masu sana’ar dowulodin da ke tura wasu fina finai na batsa”, in ji shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!