Kiwon Lafiya
Majalisar dattawa ta bawa sufeto janar wa’adi kan bincikar kashe-kashen jihar Benue
Majalisar Dattawa ta baiwa sufeto Janar na ‘yan-sandan kasar nan Ibrahim Idris wa’adin kwanaki goma sha hudu da ya bincika ya kuma kama wadanda ke da hannu cikin kashe-kashen da ke faruwa a jihar Benue domin gurfanar da su gaban kuliya.
Hakan ya biyo bayan amincewa da sakamakon rahoton kwamitin karta-kwana da majalisar ta kafa domin sake nazarin harkokin tsaro a kasar nan.
A juma’ar makon jiya ne dai kwamitin wanda ke karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye Sanata Ahmed Lawan, ya kai ziyara jihar Benue domin gano dalilan da suke janyo rasa rayuka da ake samu a jihar.
Da yake gabatar da sakamakon rahoton Sanata Ahmed Lawan, ya ce; lamarin ya yi kamarin da ke bukatar daukin gaggawa a don haka ya bukaci ‘yan-sanda da su kara kaimi wajen magance matsalar cikin kankanin lokaci.
Majalisar ta kuma bukaci rundunar ‘yan-sandan kasar nan da jami’an tsaron sirri na DSS da kuma hukumar tsaro ta civil defence da su tabbatar da cewa sun kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya.