Labarai
Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta binciko mayakan Boko-haram da suka tsere daga dajin Sambisa
Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki ko mayakan Boko-haram da suka tsere daga dajin Sambisa da kuma mayaka da suka tsere daga kasar Libya na da hannu cikin kashe-kashen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma a jihar Benue.
Shugaban kwamitin kula da harkokin ‘yan-sanda na majalisar Sanata Abu Ibrahim ne ya yi wannan kiran yayin zantawar sa da manema labarai a Abuja.
Ya ce gudanar da bincike kan lamarin ya zama wajibi sakamakon irin muggan makamai da maharan ke amfani da su wanda ya ce a iya saninsu Fulani makiyaya basa amfani da bingigogi kirar AK47.
Sanata Abu Ibrahim ya ce bako shakka yakamata a binciki wannan lamarin, domin akwai kanshin gaskiya wajen zargin cewa mayakan Boko-Haram da sojoji da suka tsere daga kasar Libya na da hannu cikin kashe-kashen.
Ya kuma ce wajibi ne sufeto Janar na ‘yan-sanda Ibrahim Idris da sauran jami’an tsaro su fadada komar bincikensu domin gano gaskiyar wadanda ke da hannu cikin kashe-kashen.