Labarai
Majalisar dattijai Najeriya ta roki kungiyar kwadago dakatar da yajin aikin da suke yunkurin shiga
Majalisar dattijan kasar nan ta roki kungiyar kwadago ta kasa NLC da ta dakatar da shirinta na tsunduma yajin aikin gama-gari don nuna fushi kan jan kafar da ake samu dangane da biyan mafi karancin albashin naira dubu 30.
Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya yi wannan kira a jiya Laraba lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar kwadagon ta NLC karkashin jagorancin shugabanta na kasa Ayuba Waba da kuma takwarorinsu na ma’aikatan majalisu PASAN karkashin Sunday Sabiyi a ofishinsa.
Sanata Ahmad Lawan ya bukaci a samu hadin kai da nuna kishin kasa, la’akari da cewa tuni ma wasu Jihohin suka fara biyan sabon mafi karancin albashin.
A na sa jawabin shugaban kungiyar kwadagon ta NLC Ayuba Waba, bayyana goyon bayan kungiyar ya yi ga duk wani yunkuri da majalisun dokokin kasar nan ke yi wajen ciyar da kasar nan gaba, sannan ya taya sanata Ahmad Lawan murna kan zabarsa da aka yi a matsayin shugaban majalisar dattijan.
Tun da fari a jawabinsa shugaban PASAN Sunday Sabiyi ya roki majalisar da ta tabbatar daaiwatar da aiwatar dokar nan ta shekarar 2018 da ta amince da biyan kashi 28 na kudin ariyar ma’aikatan majalisar.