Connect with us

Labarai

Majalisar dattijai za ta amince da kasafin 2022 da aka gabatar mata

Published

on

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce majalisar dokokin ƙasar nan za ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2022 kafin ƙarshen zaman majalisar a wannan mako.

Ahmad Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja loacin da yake gabatar da lacca a wani taro da cibiyar nazarin majalisun dokoki da dimokaradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya.

A cewarsa, majalisar mai ci a halin yanzu na yin ƙoƙari wajen gabatar da kasafin kuɗin kafin ƙarshen watan Disamba na kowacce shekara, domin ganin an fara aiwatar da shi a watan Janairu.

Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2022 da ya kai naira tiriliyan 16 da biliyan 39 mai taken ‘kasafin bunkasar tattalin arziki’.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!