Labarai
Majalisar dattija ta tabbatar da nadin alkalan Kotun koli guda 11
Majalisar dattijai, a yau Alhamis, ta tabbatar da nadin alkalai 11 na kotun koli, bayan tantance su da kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a da kare hakkin bil’adama ya yi wanda Sanata Mohammed Monguno na Jam’iyar APC bangaren Borno ta Arewa ya jagoranta.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya aike da sunayen alkalan zauren majalisar bisa shawarar da majalisar shari’a ta kasa ta bayar, don cike guraben guraben Alkalam da suka yi ritaya daga aiki.
Alkalan kotun kolin da aka tabbatar sun hada da Mai shari’a Haruna Tsammani na Arewa maso gabas, wanda a baya ya jagoranci kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, sai Mai shari’a Moore Adumein na Kudu maso Kudu da Mai Shari’a Jummai Sankey ta Arewa ta Tsakiya da Mai Shari’a Chidiebere Uwa ta Kudu maso Gabas da kuma Mai shari’a Chioma Nwosu Iheme dake Kudu maso Gabas.
Sauran alkalan da aka nada sun hada da Justice Obande Ogbuinya a Kudu maso Gabas da Mai Shari’a Stephen Adah a Arewa ta Tsakiya da Mai Shari’a Habeeb Abiru a Kudu maso Yamma, sai Mai Shari’a Jamilu Tukur a Arewa maso Yamma da Mai Shari’a Abubakar Umar a Arewa maso Yamma, sai kuma Mai Shari’a Mohammed Idris Arewa maso Yamma.
You must be logged in to post a comment Login