Connect with us

Labarai

Majalisar datijjai ta amince da tabbatar da nadin manyan alkalan kotun koli

Published

on

Majalisar dattijai

Majalisar datijjai ta amince da tabbatar da nadin manyan alkalan kotun koli su 8.

A dai makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar datijjan wasikar neman sahalewar su kan nada alkalan wanda shugaban majalisar Ahmad Lawan ya karanta a ya yin zaman majalisar a dazun nan.

A cewar wasikar shugaban kasar  ya ce nadin ya biyo bayan shawarwarin da majalisar kula da al’amuran shari’a ta kasa ta bayar kan nadin na su.

Wasikar ta shugaban kasa ta bayyana  cewar matakin nadin ya yi dai-dai ta sashi na 231 na cikin kundin tsarin mulkin kasar nan na shekara ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima

Daga cikin wadanda aka nada akwai Lawal Garba daga Arewa maso yamma da Hellen Ogunwumiju daga kudu maso yamma da Abdu Aboki daga Arewa maso yamma da kuma M M Saulawa shima daga Arewa maso yamma.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,764 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!