Labarai
Majalisar dinkin duniya ta bisa yadda mazauna kauyen Rann da ke fama da kalubalen agajin gaggawa
Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwa kan yadda mazauna kauyen Rann da ke gabashin jihar Borno ke fama da kalubalen agajin gaggawa, la’akari da cewa yawan su ya haura dubunnai.
Wannan na zuwa ne biyo bayan hare-haren da aka kaddamar a yankin na Rann da ke da tazarar kilomita goma da kasar Kamaru.
Babban jami’in majalisar dinkin duniya da ke sanya idanu kan al’amuran bayar da agaji a Najeriya, Mista Edward Kallon ne ya bayyana hakan, tare da cewa rashin kai agaji da kuma sanya idanu a yankin yadda ya kamata na daga cikin abinda ya sabbaba harin ranar 14 ga watan Janairun wannan shekara da aka kai sansanin soji.
A cewar sa a dai-dai lokacin da aka kai wannan harin, mutane sama da dubu saba’in da shida ne ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin na Rann.
Mista Kallon ya kuma tabbatar da cewa a yayin harin, an lalata cibiyar lafiya, dakunan ajiyar abinci da kuma wuraren ajiye kayayyakin kiwon lafiya hadi da wuraren kwanan jami’an lafiya, baya ga kona kasuwa da kuma wasu wurare da ke sansanin da maharani suka lalata.
A cewar sa harin na Rann ya tilastawa wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar tserewa kasar Kamaru, inda yace yankin a yanzu haka na bukatar kulawar gaggawa.