Kiwon Lafiya
Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da harin da ‘yan bindiga a jihar Kaduna
Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a wani kauye da ke yankin karamar hukumar birnin Gwari a jihar Kaduna wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Babban sakatare Janar na majalisar Antonio Gutteres ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya fitar jiya a shalkwatar hukumar da ke birnin Washington DC.
Antonio Gutteres ta cikin sanarwar dai ya kuma ce ya zama wajibi hukumomi a kasar nan su zakulo wadanda ke da hannu cikin lamarin domin gurfanar da su gaban kuliya.
Sanarwar ta kuma ruwaito Antonio Gutteres na jajantawa iyalai da ‘yan uwan wadanda lamarin ya shafa.
A ranar Asabar din makon jiya ne dai wasu ‘yan bindiga suka hallaka mutane sama da saba’in a kauyen Gwaska da ke yankin karamar hukumar birnin Gwarin jihar Kaduna.