Labarai
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Isra’ila da kashe yara a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi hukumomin Isra’ila da jami’an tsaron ta da kashe yara a Gaza da gangan, tare da bayyana hakan a matsayin wani shirin kisan kare dangi da nufin lalata makomar Falasdinawa.
Hukumar ta bayyana cewa akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa jami’an tsaron Isra’ila na kai hari kan yara da gangan ta hanyar amfani da makamai masu linzami, jirage marasa matuka, da kuma harbin bindiga kai tsaye.
Binciken ya kammala da cewa wadannan hare-hare na da tsanani da kuma yawa har sun kai matsayin laifuffukan yaki, laifuffuka kan bil’adama, da kuma kisan kare dangi wanda ke barazana ga rayuwa da makomar Falasdinawa a Gaza.
Rahotanni na baya-bayan nan daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya kamar OCHA sun nuna cewa al’ummar yankin na fuskantar matsaloli daban-daban na rayuwa.
Adadin motocin kayan abinci da magunguna da ke shiga Gaza ya ragu sosai, da a yanzu motoci 50 zuwa 60 ne kawai ke shiga a kullum, sabanin motoci 600 da ake bukata.
You must be logged in to post a comment Login