Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta rufe gidan daukar fina-finai a Dorayi

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe Gidan daukar shirin fina-finai a Unguwar Bello da ke Dorayi Karamar Hukumar Gwale wanda jarumin masana’antar Kannywood Sultan Abdurrazak ya samar.

Da ya ke zantawa da manema labarai Jim kadan Bayan rufe Gidan shugaban kwamitin kar-ta-kwana mai aikin dakile gine-gine da Ba su cika ka’ida ba, kuma shugaban riko na Hukumar tsara Birane ta Jihar Kano Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ya ce Gurin zai cigaban da Zama a rufe har sai Gwamnati tayi nazari.

Sai dai wasu matasa a Unguwar ta Dorayi sun nuna rashin goyon bayansu kan rufe gidan.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da bibiyar duk wani ginin da ya dakatar ko kuma wanda ake yinsa ba bisa doka ba, domin daukar matakin da ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!