Labarai
Majalisar dokoki ta yarje wa Abba Gida-Gida ciyo bashin Biliyan 4
Majalisar dokokin jihar Kano, ta sahale wa Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, damar karɓar bashi maras ruwa na Naira biliyan huɗu daga Babban bankin ƙasa CBN.
Majalisar, ta sahale ciyo bashin ne a zamanta na yau Juma’a biyo bayan wasiƙar da gwamnan ya aike wa majalisar wadda shugabanta Jibril Isma’il Falgore ya karanta jim kaɗan bayan da gwamnan ya gabatar da ƙunshin Kasafin kuɗin baɗi.
Ta cikin wasiƙar gwamnan ya ce, zai yi amfani da bashin ne wajen ƙarasa aikin samar da tashoshin lantarki mallakin jihar Kano a madatsun ruwa na Challawa da Tiga.
Da yake ƙarin haske kan wasiƙar, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ya buƙaci mambobin majalisar da su amince da ciyo bashin kasancewarsa maras ruwa kuma aikin zai taimaki al’umma.
You must be logged in to post a comment Login