Jigawa
Majalisar Dokokin Jigawa ta amince da karin kasafin Naira biliyan 58

Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta amince da karin kasafin kudi na Naira biliyan 58 da gwamnatin jihar ta gabatar mata.
Wannan na zuwa ne bayan majalisar ta amince da rahoton kwamitin kudi na majalisar.
Shugaban kwamitin, Ibrahim Hamza-Adamu, ya ce karin kasafin kudin ya biyo bayan karin kudaden shiga da ake sa ran jihar za ta samu daga asusun gwamnatin tarayya.
Ya bayyana cewa, kasafin kudin na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 698.3, kuma da wannan karin, kasafin kudin zai kai Naira biliyan 756.3.
Hamza-Adamu ya bukaci majalisar da ta tabbatar da sa ido yadda ya kamata, domin tabbatar da amfani da kudaden a wuraren da aka amince da su.
You must be logged in to post a comment Login