Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bukaci a tilastawa ‘yan kwangila kammala ayyukansu
An bukaci dan kwangilar dake aikin Titin Sheikh Mudi Salga a yankin karamar hukumar Dala da ya koma bakin aikin don kammala aikin cikin lokaci.
Majalisar dokokin jihar Kano ce ta bukaci hakan, biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, Alhaji Lawan Hussaini, ya gabatar a zaman majalisar na ranar 27 ga watan Yulin 2021.
Dan majalisar ya ce, kimanin shekaru biyar kenan da fara aikin amma kawo yanzu bai fi kaso daya cikin uku aka kammala ba.
Ya kuma ce, rashin kammala aikin ya jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali.
Haka shi ma takwaransa na karamar hukumar Kiru, Alhaji Kabiru Hassan Dashi ya gabatar da kudurin gaggawa na kira ga gwamnati da ta sanya a kammala aikin Titin da ya tashi daga gadar karkashin kasa ta hanyar fanshekara zuwa yankunan Madobi da Kiru.
Dan majalisa mai wakiltar Doguwa, Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad shi ma ya gabatar da kudurin neman daukin gwamnati kan aikin gyaran wata hanya da ake yawan samun hadurra a yankin.
Doguwa ya ce ko a makwan da ya gabata sanadiyar ambaliyar ruwa a hanyar fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu.
You must be logged in to post a comment Login