Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta bukaci gwamnati ta gaggauta kai wa mutanen Bichi dauki bisa afkuwar ambaliya da Iska

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta kai dauki ga al’ummar Karamar Hukumar Bichi da ambaliyar Ruwan Sama da Iska ya shafa.

 

Bukatar ta biyo bayan kudurin gaggawa da dan majalisar mai wakiltar mazabar Bichi, Lawan Shehu, ya gabatar a zaman majalisar da shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranta.

 

Lawan Shehu ya ce iftila’in da ya afku a ranar Alhamis din da ta gabata ya yi sanadin mutuwar mutane takwas tare da lalata gidaje da dukiyoyin da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

 

Dan majalisar ya kuma yi kira ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta samar da kayan agajin gaggawa da sauran tallafin da za su taimaka wa wadanda wannan ibtila’i ya shafa.

 

Bayan muhawara kan kudirin, Majalisar ta amince da shi baki daya tare da bukatar gwamnatin jihar ta hanzarta kai agaji da tallafin da ya dace ga dukkan wadanda abin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!