Labarai
Majalisar dokokin Kano ta dawo daga hutu
Majalisar dokoki ta jihar Kano, ta bukaci al’ummar jihar da su cigaba da bata goyon baya wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyanta domin ciyar da jihar gaba.
Shugaban majalisar Abdul’aziz Garba gafasa, ne ya bukaci hakan yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar na yau Talata da ta dawo zama bayan tsawon lokaci da ta shafe tana hutu.
Shugaban majalisar ya kuma yabawa mutanen jihar Kano bisa yadda suke zabo wakilan da suke ganin sun yadda su wakilce su a zauren majalisar, yana mai cewa hakan yana taimakawa jihar Kano wajen samun ayyukan more rayuwa.
Za’a bude makarantu a Najeriya
Buhari zai rabawa manoma bashi- Sabo Nanono
A dai zaman majalisar na yau, dakatattun mambobin majalisar 5 sun koma bakin aiki bayan da suka dauki tsawon lokaci basu samu damar hakan ba har sai da suka samu izinin kotu na mayar da su tare da biyan dukkan hakkokinsu.
Da yake jawabi a madadin ‘yan majalisar 5, wakilin kananan hukumomin Rimin Gado da Tofa Muhammad Bello Butu-butu, ya bayyana cewa, komawar tasu majalisa ya tabbatar da cewa, ana bin umarnin kotu da kundin tsarin mulkin kasa.
Wakilinmu Auwal Hassan Fagge ya ruwaito cewa, a zaman majalisar na yau gwamnatin jihar Kano ta aike da takardar neman majalisar ta tantance Ahmad Rufa’i Yalwa domin nada shi a matsayin kwamishina a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC.
You must be logged in to post a comment Login